Ƙungiyar Miyetti Allah ta ta buƙaci gwamnatin Najeriya da ta ɗauki mataki a kan mutanen da ke halaka Fulani makiyaya a kudancin ƙasar.

Mai Magana da yawun ƙungiyar Sakeh Alhassan ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunaw ad aya yi da jaridar Punch.
Hakan na daga cikin martanin da yayi a kan ƙungiyar nan mai rajin kafa ƙasar BIAFRA wato IPOB bayan kashe wani babban jigo a cikin ta.

Ya ce a cikin wata guda an kashe Fulani makiyaya guda 50 a kudu maso gabashin ƙasar.

Sannan ya yabawa jami’an tsaro a bisa ayyukan su tare da buƙatar hukunta duk wanda aka samu da kashe Fulani makiyaya a ƙasar.
Kudu maso gabashin Najeriya, na daga cikin jihohin da wasu gwamnonin su ka haramta kiwo tare da umartar Fulani da su fice daga jihohin.