Babbar  jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta zargi gwamnatin shugaba Buhari da nuna halin ko in kula da ake a ƙan ƴan ƙasar.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne a yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

Cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun jam’iyyar Kola Ologbodiyan ya fitar, ya zargi shugaban ƙasa da gwamnatin sa a bisa ƙin fitowa fili don yi w al’umma jawabi, tare da ƙoƙarin ɗaukar matakin da ya kamata don magance matsalar.

Jam’iyyar PDP ta ce alamu ne na gazawar gwamnatin ganin yadda ta yi burus da halin da al’ummar ƙasar ke fuskanta na rashin tsaro.

A cewar babbar jam’iyyar Adawar, abin da gwamnatin jam’iyyar APC ta fi mayar da hankali a yanzu shi ne yadda za su lashe zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.

Ta ce rashin mai da hankali a kan al’amuran da su ke damun ƴan ƙasar, shi yak e sa ƴan bindiga ke ci gaba da cin Karen su babu babbaka a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: