Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ƴan Sanda Sun Kama Mutane Huɗu Da Kisan Yaro Mai Shekaru Shida

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta kama wau mutane huɗu da ake zargi da kisan wani yaro mai shekaru shida bayan sun yi garkuwa da shi kuma su karɓi kudin fansa.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ASP Muhammad Jalige ne ya bayyana hakan a yayin da yake hoken su ga ƴan jaridu a madadin kwamishinan ƴan sandan jihar.

A binciken da yan sanda su ka yi sun gano cewar maƙocin su yaron ne ya sace shi a unguwar Badarawa sannan su ka kais hi Kano su ka kashe shi bayan sun karɓi kudin fansa naira miliyan guda.

Tun da farko mahaifin yaron ne ya kai ƙorafin gurin ƴan sanda sannan su ka fara gudanar da bincike a kai daga ranar 29 ga wtaan Afrilun da ya gabata.

Daga cikin mutanen da aka kama akwai maza uku mace guda ɗaya.

Rundunar ta shawarci iyaye da su dinga sa ido a kan ƴayan su da kuma wadanda su ke mu’amala da su don gudun faruwar makamancin haka a nan gaba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: