Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya DSS ta yi gargaɗi ga malamai da ƴan siyasa da suke kalaman tayar da hankali a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta ce ba za ta ci gaba da kawar da kai a kan kalaman wasu mutane da za su iya tayar da hankali a ƙasar ba.

Hukumar ta ce abin da ya ja hankalin su shi ne kalaman da wasu key i na tumbuƙe gwamnati ko kuma kalaman tunziri wand ahakan ka iya haifar da rashin zaman lafiya a ƙasar.

Hukumar ta zargi mutanen da ke yin irin kalaman da cewar sun a yi ne domin biyan buƙata ta ƙashin kan su.

Sannan sanarwar ta ƙara da cewar duk da kasancewa mulkin damokaradiyya ya bayar da damar faɗar albarkacin baki, hakan ba yana nufin kowacce kalma mutum zai iya furtawa ba.

A cewar hukumar, mafi yawan kalaman da ya ja hankalin shi su ne yadda ake yin kalaman da ke barazana ga gwamnati da kuma ɗorewar zaman lafiya a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: