Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun kai hari wasu ƙauyuka a jihar Neja tare da awon gaba da mutane da dama.

Wasu mazauna garin Shadaɗi sun bayanawa BBC cewar mutanen da aka sace sun kai su 100.

Yayin da ƴan bindigan su ka kai harin an kashe mutane sama da dama sai dai gwamnatin ta musanta adadin mutanen da aka ambata.

A sakamakon harin, dubban mutane sun tsere daga muhallin su sanadin fargabar da suke ciki a garin.

Kwamishinan tsaro a jihar Alhaji Sani Idris ya tabbbatr da faruwar lamarin, sai dai y ace adadin mutanen da aka sace bai kai 100 ba.

A kwana nan ake zargin mayaƙan Boko Haram sun shiga jihar Neja tare da ƙoƙarin kafa sansanin su a cikin dazukan jihar.

Sai dai babu tabbacin ko mayaƙan Bokjo Haram ne su ka kai harin ko kuma masu garkuwa da mutane ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: