Rahotanni daga ƙasar Indiya na tabbatar da cewar cutar Korona ta kashe mutane sama da dubu huɗu a ƙasar.

Hakan na zuwa ne bayan da cutar da shiga ƙauyukan a wasu jihohin ƙasar.

Wannan ne karo na farko da aka samu mafi yawan mutane da cutar ta hallaka a cikn awanni 24.

A sakamakon hakan wasu daga ciin shugabanni a jihohin su ka saka dokar kulle domin rage yaɗuwar ta.

A na sa ran cutar za ta ƙara kisa fiye da hakan a nan gaba, sanadin ƙauyukan da ta shiga ba su da ingantaccen kiwon lafiya da kuma ilimin da zai hana yaɗuwar ta.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: