Daga masu kishin Kano

A sakamakon labarai da wasu jaridu su ka wallafa na rikin cikin gida wanda ya kunno kai a tsagen siyasar kwankwasiyya, wasu daga ciki sun huce haushin su a kan Mallam Abba Anwar babban sakataren yada labarai na mai girma gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.
Wannan wani al’amari ne da ake kira tabarmar kunya wai da hauka ake naɗe ta.

Duk da kasancewa jaridun da su ka wallafa ba su da alaƙa da Mallam Abba Anwar amma idon mutanen ya rufe tare da caccakar sa a shafukan sada zumunta.

A tsari na gaskiya idan har ya kasance labarin ba gaskiya bane ai akwai mutanen da aka gani su bayyana a faifan bidiyo tare da nuna alamu na rikicin.

Ba wani sabon abu bane tunda ba ku kawo hujjar da za ta ƙaryata labarin ba.

Labari gaskiya ne abinda jaridun su ka wallafa haka yake tunda babu wani da ya fito fili ya musanta illa mutanen da ke yi sagarabtu a kafafen sada zumunta.

Siyasa ba gaba bace sannan ba hanya ce ta cin mutunci ba ya zama wajibi mu duba hanyar da jihar Kano za ta ci gaba ba tare da nuna wariya ba.

Abinda Abba Anwar kawai ya yi shi ne yaɗa labari, kuma shikenan sai ku ce ƙarya ne? To idan ƙarya ne ai ba shi za ku ƙaryata ba jaridun da su ka wallafa za ku ƙaryata shi ma sai da hujjar ƙaryatawar.

Ku daina yaudarar kanku ana juyaku yadda ake so, mu fuskanci yadda Kano za ta ci gaba ba wai kura da shan bugu gardi da kwashe kuɗi ba

Mallam Abba Anwar kwararren ɗan jarida ne da ya san aiki, kuma duk da yana cikin gwamnati ba zai yi wani abu da zai karya mutuncin aikin jarida ba.

Na ji wai har da cewa za a binciko labari sabo a kan Abba Anwar, to ai ita gaskiya guda ɗaya ce, Abba Anwar dai ba ƙazafi ya yi muku ba kuma babu wani abu da za ku binciko sai idan sharri za ku yi masa.

Maƙurar sharrin da za ku yi masa a ce ya yiwa wata ciki, ko tsohon ɗan tatsine ne ko kuce an taɓa kamashi yana harkar banza da wani ko kuma ɗan shi’a ne ko ya ci kuɗin gwamnati to daga nan kuma sai me? duk girman sharrin da za ku yi ba zai wuce wannan ba.

Wani rashin wayo da u ka nuna ma shi ne ci gabba da yaɗa labarin wai da sunan zagin Abba Anwar, wannan ai burmawa ciki wuƙa ne.

Da za ku yi adalci shi fa Abba Anwar bai taɓa shiga sabgar siyasa ba, kuma babu wani da ya taɓa yi da zai nuna wani abu illa iyaka aikin sa kawai muka san yana yi.

Yaɗa labari ba shi zai sa ace labari ƙarya bane sai idan har mutanen da aka lissafa da maganganunsu sun ƙaryata kansu da kansu.

Rikicin Kwankwasiyya – Ƴan Kwankwasiyya Sun Huce Haushin Su A Kan Hadimin Ganduje Mallam Abba Anwar

Daga masu kishin Kano

A sakamakon labarai da wasu jaridu su ka wallafa na rikin cikin gida wanda ya kunno kai a tsagen siyasar kwankwasiyya, wasu daga ciki sun huce haushin su a kan Mallam Abba Anwar babban sakataren yada labarai na mai girma gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.
Wannan wani al’amari ne da ake kira tabarmar kunya wai da hhauka ake naɗe ta.

Duk da kasancewa jaridun da su ka wallafa ba su da alaƙa da Mallam Abba Anwar amma idon mutanen ya rufe tare da caccakar sa a shafukan sada zumunta.

A tsari na gaskiya idan har ya kasance labarin ba gaskiya bane ai akwai mutanen da aka gani su bayyana a faifan bidiyo tare da nuna alamu na rikicin.

Ba wani sabon abu bane tunda ba ku kawo hujjar da za ta ƙaryata labarin ba.

Labari gaskiya ne abinda jaridun su ka wallafa haka yake tunda babu wani da ya fito fili ya musanta illa mutanen da ke yi sagarabtu a kafafen sada zumunta.

Siyasa ba gaba bace sannan ba hanya ce ta cin mutunci ba ya zama wajibi mu duba hanyar da jihar Kano za ta ci gaba ba tare da nuna wariya ba.

Abinda Abba Anwar kawai ya yi shi ne yaɗa labari, kuma shikenan sai ku ce ƙarya ne? To idan ƙarya ne ai ba shi za ku ƙaryata ba jaridun da su ka wallafa za ku ƙaryata shi ma sai da hujjar ƙaryatawar.

Ku daina yaudarar kanku ana juyaku yadda ake so, mu fuskanci yadda Kano za ta ci gaba ba wai kura da shan bugu gardi da kwashe kuɗi ba

Mallam Abba Anwar kwararren ɗan jarida ne da ya san aiki, kuma duk da yana cikin gwamnati ba zai yi wani abu da zai karya mutuncin aikin jarida ba.

Na ji wai har da cewa za a binciko labari sabo a kan Abba Anwar, to ai ita gaskiya guda ɗaya ce, Abba Anwar dai ba ƙazafi ya yi muku ba kuma babu wani abu da za ku binciko sai idan sharri za ku yi masa.

Maƙurar sharrin da za ku yi masa a ce ya yiwa wata ciki, ko tsohon ɗan tatsine ne ko kuce an taɓa kamashi yana harkar banza da wani ko kuma ɗan shi’a ne ko ya ci kuɗin gwamnati to daga nan kuma sai me? duk girman sharrin da za ku yi ba zai wuce wannan ba.

Wani rashin wayo da u ka nuna ma shi ne ci gabba da yaɗa labarin wai da sunan zagin Abba Anwar, wannan ai burmawa ciki wuƙa ne.

Da za ku yi adalci shi fa Abba Anwar bai taɓa shiga sabgar siyasa ba, kuma babu wani da ya taɓa yi da zai nuna wani abu illa iyaka aikin sa kawai muka san yana yi.

Yaɗa labari ba shi zai sa ace labari ƙarya bane sai idan har mutanen da aka lissafa da maganganunsu sun ƙaryata kansu da kansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: