Fadar masarautar Daura ta sanar da soke da bikin hawan ƙaramar sallah a bana.

Masarautar ta soke bikin hawan ƙaramar sallah ne sakamakon fargabar tsaro da ake fuskanta a Najeriya.
Galadiman Daura Alhaji Ahmadu Diddiri Ahmadu ya tabbatar da hakan wanda ya ce an yi hakan ne domin tsare rayuka da lafiyar al’umma.

Sannan ya ce za a yi addu a ta musamman a kan neman zaman lafiya a ƙasar da zarar an idar da sallar idi.

Manufar hakan shi ne neman zaman lafiya mai dorewa tare da neman ci gaba a ƙasa baki ɗaya.
A jihar Neja ma an soke bukukuwan idin ƙaramar sallah a bana sakamakon fargabar taɓarɓarewar tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.