Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a Najeriya ta yi gangami na musamman domin tinkarar bukin ƙaramar sallah a ƙasar.

Mai Magana da yawun hukumar a ƙasar Bisi Kazeem ne ya ce sun ware jami’an su su 35,000 da kuma motoci guda 720 sai motar ɗaukar mara lafiya guda 120 duka domin tinkarar bikin ƙaramar sallah a Najeriya.
Haka kuma na ware manyan motoci guda 25 da baburan guda 200 za su fara aiki na musamman ne daga gobe Talata zuwa ranar 17 ga watan da muke ciki.

Kakakin hukumar ya ƙara d acewar jami’an nasu za su tabbatar an yi amfani da tituna a Najeriya yadda ya dace da kuma tabbatar da bin ƙai’dar da aka saka don hana kamua da cutar Korona.

Ya ƙara da cewa a dukkan wasu bukukuwa da ake yi a ƙasar rundunar na yin shiri na musamman domin tabbatar da bin doka ba iya bikini di kadai ba.
Sannan za a mai da hankali wajen zuba jami’an a manyan titunan da suka haɗa jihohi daban-daban domin tabbatar da kiyaye doka.