Ƙasar saudiyya ta sanar da cewar akwai yuwuwar gudanar da aikin hajji a bana amma bisa wasu sharruɗa da su ka saka.
Ma’aikatar aikin hajji a ƙasar ce ta sanar da hakan wadda ta bayyana cewar za ta sanar da matakan da za a bi don gudnar da aikin hajjin bana.
A shekarar da ta gabata an ƙayyade wasu tsirarun mutane domin yin aikin hajjin sakamakon cutar Korona wadda ta sauya al’amura masu yawa a duniya.
Idan ba a manta ba a shekarar bar aba a bar wasu sun yi aikin hajji daga wasu ƙasashen b illa waɗanda su ke zaune a ƙasar.
A bana kuwa an gudanar da sallar tarawih da masallatan harami wanda aka bar mutane daga ƙasashe daban-daban don yin umara.
A na sa ran za a ƙara adadin mutanen da za su yi aikin hajjin fiye da mutanen da su ka yi umara a bana.