Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da ranakun Laraba da ALhamis matsayin ranar hutun idin ƙaramar sallah.

Ministan harkokin cikin gida Ra’uf Adegbeson ne ya sanar da hakan a daren ranar Litiinin.
Ministan ya taya al’ummar musulmin ƙasar murnar bikin ƙaraamr sallah tare da kira ga al’umma da su yi amfani da damar wajen yi wa ƙasa addu’a a bisa hain da take ciki.

A sanarwar da babban sakataren hukumar Dakta Shu’aib Belgore ya buƙaci a saka batun tattalin arziƙi a cikin addu’a domin fatan farfadowar sa.

Sannan ya roƙi al’ummar kasar da su kasance masu bin dukoki tare da ƙaunar juna bisa koyarwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Sannan ya tabbatar da cewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na shirin kawo ƙarshen dukkan ta’addancin da ke damun ƙasar.
Haka kuma ya sake nanata cewar duk ɗan Najeriya na da ƴancin watayawa ko rayuwa a duk inda yake so na faɗin ƙasar ba tare da firgici ko tsoro ba.
