Hukumar lura a tuƙi a jihar Kano Karota ta yi gargaɗi gamasu ɗabi’ar tuƙin gannganci a yayin bikin salla.

A sanarwar da mai Magana da yawun hukumar Nabilisi Abubakar K/Na’isa ya fitar, hukumar ta ce a shirye ta ke domin kama dukkan wani da ya karya dokar tuƙi a jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewar hukumar ta shirya jami’anta guda dubu daya, waɗanda za su yi aiki da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da hana afkuwar cunkoso a faɗin jihar.

Sannan hukumar ta ce za ta tabbatar an bi dukkan dokar tuƙi a jihar domin hana afkuwar cunkoso ko haifar da haɗdura a titunan jihar.

Daga cikin abubuwan da hukumar za ta sanya idanu domin ganin an hana afkuwarsu akwai tuƙin ganganci da gudun wuce sa’a wanda hakan ke kaiwa ga rasa rayuka.
Hukumar ta jaddada cewar a shirye take domin kama duk wanda ta samu da aikata laifin sannan a yanke masa hukunci kamar yadda kundin dokar hukumar ya bayar da dama.