Masu garkuwa da mutane sun saki wata yan jarida wadda aka sace a Adamawa bayan biyan kudin fansa.

An sace Amra Ahmed Diska gidanta a ranar Talata 4 ga watan mayun da muke ciki, kimanin kwanaki takwas kenan.
An saketa a jiya Laraba bayan biyan kudin fansa kamar yadda mijinta Alhaji Ahmed Mbaba ya bayyana.

Amra Ahmed ƴar jarida ce da ke aikin tace labarai a kafar yada labarai ta Adamawa Broadcasting Corporation.

Sai dai mijin bai bayyana adadin kudin da aka biya masu garkuwan kafin sakin matar tasa ba.
Bayan sace ta, ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa reshen jihar Adamawa ta shirya addu a ta musamman domin ganin ta kuɓuta daga hannun masu garkuwan.
Garkuwa da mutane dai tuni ya zama ruwan dare wanda ya karaɗe wurare daban-daban na Najeriya.