Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar musulmi da su sanya ƙasar a cikin addu a yayin da ake bikin ƙaramar sallah a ƙasar da wasu ƙasashen duniya.

A wani saƙo da ya aikewa manema labarai, shugaban ya buƙaci a sanya ƙasar a addu’a sanadin ayyukan masu garkuwa da mutane da kashe-kashe da sairan hare-haren da ake kai wa a wurare daban-daban na fadin kasar.
Sannan ya buƙaci al’ummar ƙasar mabiya addinin musulunci da mabiya addinin kirista da su ƙaunaci juna tare da haɗa kai.

A cewar shugaban, hadin kan musulmi da kirista a wannan lokaci na da matuƙar muhimmanci duba ga ƙalubalen da ƙasar ke ciki a yanzu.

Shugaba Buhari ya buƙaci shugabannin addini da na siyasa da masu riƙe da sarautar gargajiya da su ja hankalin ƴan jama’a don ganin sun tausayawa junansu.
Muhammadu Buhari ya gudanar da sallar idin sa a gida tare da iyalansa da sauran ministocin sa a Abuja.