“Ko a masallacin Makka da Madina ma an yanka filaye an gina shaguna” a cewar Ganduje.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya wanke sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a bisa zargin siyar da wasu filaye daga cikin masallacin Idi.

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar, gwamnan ya bayyana cewar sarkin ya yi hakan ne a bisa ƙa’ida kamar yadda su ka tabbatar.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a yayin bikin hawan sallar na Nassarawa yayin da sarkin Kano Alhji Aminu Ado Bayero ya kai masa ziyara a gidan gwamnati.

Gwamna Ganduje ya ƙalubalanci masu maganganu a kan siyar da wani ɓangare na masallacin, wand agwamnan y ace ko a masallatan Makkah Da Madina an yanka wasu wuraren da aka gina shaguna a ciki.

Sannan gwamnan ya aike da saƙon shugaban ƙasa a kan ƙulla alaƙar aiki tsakanin masarautar Kano da sauran masarautu a Najeriya.

A yayin da yake jawabi sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yabawa gwamnatin Kano, tare da tabbatar da cewar masarautar sa da sauran masarautu hudu na jihar za su ci gaba da bayar da goyon baya domin samun nasarar gwamnatin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: