Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana cewar jami’an tsaro na buƙatar sabbin makamai da kuma horo na musamman.

Tsohon shugaban ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samarwa da sojoji makamakn yaƙi na zamani tare da shirya musu sabon horo domin tinkarar matsalar tsaron da ake ciki.

A cikin wata hira da yay i da BBC Hausa janar Babangida y ace ya kamata al’ummar ƙasa su marawa gwamnati da sojojin baya domin magance matsalar.

Ya ƙara da cewar bayan samarwa da sojojin sabbin makaman yaƙi na zamani ya kamata a horar da su yadda za su yi amfani da sub a wai a basu sabbin kayan aikin ba tare da sanin hanyar sarrafa sub a.

Ya ce ya bayar da shawara a kan hakan ne domin samar da mafitar da ake buƙata wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a ƙasar.

Sannan y ace akwai abubuwa da dama da aka yi ba bisa ƙa’ida ba kuma idan gwamnatin ta nutsu ta gyara za a samu sauyi a matsalar tsaron da ake fuskanta.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: