An kashe mayaƙan ne ta hanyar saka wani abin fashewa da aka saka a garin Dawuri a ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Rundunar ta samu bayanai a kan cewar mayaƙan na shirin kai wani hari Maiduguri babban birnin jihar.
A sakamakon hakan rundunar sojin ta shirya kai harin kwanton ɓauna ta hanyar saka abin fashewa a sansanin mayaƙan Boko Haram.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun taɓarbarewar tsaro a Najeriya wanda yay i sanadiyyar rasa ran dubban mutane.

A kwanakin nan mayaƙan Boko Haram siun matsa kai hare-hare wanda ya sa har wasu daga cikin mazauna wasu yankunan a jihar Borno yin hijira.
Jihar Borno ta shafe sama da shekaru goma tana fuskantar rikicin mayaƙan Boko Haram.