Ƴan bindiga a jihar Neja sun kashe sojoji biyu har lahira yayin da suka tafi da wani ɗan ƙasar china guda a wani hari da su ka kai.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a wani gari da ke ƙaramar hukumar Magama ta jihar.
Yayin da su ka kai harin sun yi ƙoƙarin kutsawa wani kamfani da ke aikin wani titi kuma su ka tafi da mutum ɗaya ɗan ƙasar China.

An yi musayar wuta tsakanin ƴan bindigan da jami’an tsaro har aka kashe sojoji guda biyu sannan aka jikkata wasu da dama.

Tuni ƴan bindigan su ka shiga cikin wani daji a garin yayin da jami’an tsaro su ka tsare hanyar don ganin sun ceti wanda aka sace.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar ta tuntuɓi kakain ƴan sanda a jihar Wasiu Abiodun kuma bai magantu a kan lamarin ba har lokacin da aka kammala hada labarin.