Shugaban ƙasar Najeriya MUhammadu Buhari na neman amincewar majalisar dattawa domin ciwo bashin naira tiriliyan 2.3.

Hakan na ƙunshe a cikin wata wasiƙa da aka aike gamajalisar wanda shugaban majalisar Ahemd Lawal ya karanto a gaban majalisar yau Talata.
Bashin da z aa ciwo cike giɓi ne na kasafin kuɗin da aka yin a shekara ta 2021 da muke ciki.

A cewar shugaban, za a yi amfani da kuɗin ne wajen gudanar damanyan ayyukan da su ka shafi ɓangaren lafiya, sufuri da ɓangaren Ilimi.

Hakan na zuwa ne wata guda bayan majalisar ta amincewa gwamnatin tarayyar ciwo bashin kuɗi dala biliyan 1.5.
Ciwo bashin da gwamnatin shugaba Buhari key i na janyo cece kuce daga bakin ƴan ƙasar.
Wanda wasu ke furta cewar basu ga ayyukan da ake yi da kudin da ake ziwowa bashi ba.