Ƙungiyar gwamnonin Najeriya sun buƙaci a mayar da litar mai zuwa naira 385 duk lita guda.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan zaman tattaunawa da su ka yi a daren jiya Laraba.
Ƙungiyar ta yi duba da shawarar da wani kwamiti na gwamnatin jihar Kaduna ta fityar a kan janye tallafin mai gaba ɗaya.
A yayin zaman, gwamnan Kaduna Mallam Nasir El’rufa’I ya bayyana cewar, duk wata gwamnatin na kashe kudin tsakanin naira biliyan 70 zuwa biliyan 210 a kan tallafin mai.
Kwamitin ya bayar da shawarar siyar da wsu matatun mai guda uku bayan an gyara su.
A halin yanzu dai ana sayar da litar mai a kan kuɗi naira 165 duk lita guda.
A baya an yi zargin gwamnain Najeriya da ƙara farashin man zuwa sama da naira 200 lamarin da gwamnatin ta musanta.