Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun sun kama wata mata da ta hallaka mijinta sanadin Tarawa da yayi da wata macen daban.

An kama matar mai suna Olanshile Nasirudden mai shekaru 47 bisa zargin hallaka mijinta a jiya Laraba.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar Ambinbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ga ƴan jarida.

Ya ce matar ta cakawa mijin nata wuƙa ne sannan ta sassara shi.

Bayan samun ƙorafin sun yi gaggawar kai mijin matar zuwa babban asibitin Ijebu-Ode kuma a nan aka tabbatar mijin yam utu.

Tuni kwamishinan yan sandan jihar ya bayar da umarni ga jami’an sa domin mayar da ƙorafin zuwa babban sashen binciken laifukan da su ka shafi kisan kai domin faɗaɗa bincike.

Da zarar sun kammala binciken za su gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu domin yanke mata hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: