Wasu ƴan bindiga sun kashe mutane 21 a jihar Zamfara.
Mutane 19 daga cikin waɗanda aka kashe an kashe su ne a ƙauyen Damaga da Dutsi a ƙanana hukumomin Maradun da Zurmi na jihar.
Mutanen sun gamu da ajalinsu ne yayin da su ka je gona don fara shirin gudanar da noma a bana.
Sai dai kafin zuwan nasu ƴan bindigan sun gargaɗi mutanen a kan zuwa gonar domin yin noma.
Baya ga mutane 19 da aka kashe an kuma kashe wasu ƴan sanda biyu a yankin Magami na ƙaramar hukumar gusau babban birnin jihar.
Mai Magana da yawun ƴan sanda ajihar SP Muhammad Shehu ya bayyana cewar, jami’an nasu biyu sun rasa ransu ne yayin da su ke ƙoƙarin daƙile wani hari da ƴan bindiga su ka kai.
Tuni kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umarnin jibge kwararrun jami’an tsaro tare da aike da su cikin daji domin magance matsalar.