A yammacin ranar Lahadi wasu ƴan bindiga su ka kai hari ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa reshen jihar Anambara tare da tare da kashe wasu mutane.

Ƴan bindigan sun sake kai hari wani ofishin ƴan sanda a Awka babban birnin jihar.
Wani shaidar gani da ido y ace ƴan bindigan sun kai harin ne a cikin wasu motoci ƙirar Hilux guda uku ɗauke da muggan makamai.

Daga zuwan su ne kuma su ka fara harbin mutane wanda yay i sanadiyyar mutuwar wasu daga ciki.

Sai dai ba a bayyana adadin mutane da su ka mutu a sanadin harin ba.
Shugaban hukumar zaɓe a jihar Nwachukwu Orji y ace ya samu labarin harin da aka kai ofishin su amma bas u gama tantance abin da ya faru ba.
Shi ma jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Anambara Tochukwu Ikenga ya bayyana cewar sun a ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Ana zargin ƴan ƙungiyar IPOB masu rajin kafa ƙasar BIAFRA da kitsa hare-hare a kudu maso gabashin Najeriya.
A makon da ya gabata sai da hukumar zaɓe a Najeriya ta yi wani zaman gaggawa a kan hare-haren da ake kai wa ofisoshinta da ke kudancin ƙasar, wanda ta ce hakan babbar barazana ce ga zaɓen 2023 mai zuwa.