Aƙalla mutane 70 ne su ka jikkata sanadin wata gobara da ta tashi a wani gidan mai a Kano.

Hukumomi a jihar Kano ne su ka bayyana hakan bayan da su ka tantance mutanen da iftila’in ya shafa.

Gobarar ta tashi ne a wani gidan mai da ke unguwar sharaɗa a Kano, har karo biyu a cewar hukumomin.

Kwamishinan ayyuka na jihar Kano Alhaji Garba Idiris Unguwar Rimi ne ya bayyana hakan wanda y ace gobarar farko ta fara ritsawa da mutane 43.

Bayan an kashe gobarar farko ne kuma ta biyu ta sake tashi wanda ya yi sanadiyyar shafar wasu daga cikin masu aikin kashe gobarar da ma’aikatan gidan man.

Sai dai wasu rahotannin na nuni da cewar adadin mutanen da gobarar ta rutsa da su sun zarce yadda mahukuntan su ka bayyana.

Tuni aka garzaya da waɗanda gobarar ta shafa zuwa asibitin kwararru na Murtala domin kula da lafiyar su.

Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta bayyana cewar ta na nan tana gudanar da bincike domin gano dalilin tashin gobarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: