Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon hafsan sojin ƙasa na Najeria.

Darankatan yaɗa labarai na hukumar sojin ƙasa Birgediya Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa yau Alhamis.
Kafin naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya shi ne shugaban rundunar yaƙi da mayaƙan Boko Haram da sauran muggan laifuka wanda ake kira Operation Haɗin Kai.

Naɗin ya zo ne kwanaki shida da rasuwar tsohon hafsan sojin ƙasar Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu sakamakon hatsarin jirgi a Kaduna.

An yi jana’izarsa da sauran waɗanda su ka rasu a Abuja ranar Asabar.
Har yanzu ba a kai ga tabbatar da dalilin faruwar hatsarin jirgin ba.