Wasu ƴan bindiga da ake zargi ƴan ƙungiyar IPOB ne sun ƙona wani ofishinyan sanda da wata kotu a jihar Imo.
Mutanen sun afkawa wata kotun majistire da ke Attah tare da ƙone ta sannan su ka lalata wani asibiti a garin.
A yau Asabar ƴan bindiga su ka fara zuwa ofishin ƴan sanda da ke Njaba su ka ƙone shi bayan sun ɗauki lokaci su na harbi kan mai uwa da wabi.
Cikin watanni uku ƴan bindiga sun kai jerin hare-hare jihar Imo, harin da ya fi ɗaukar hankali shi ne ɓalle gidan yari na jihar da helkwatar yan sanda tare da kuɓutar da ɗaurarru da ke ciki.
A na zargin ƴan ƙungiyar IPOB masu rajin kafa ƙasar BIFRA da kitsa kai hare-hare kamar yadda rundunar ƴan sanda ta yi zargi a baya.
Kudu maso gabashin Najeriya na fama da rikicin ƙungiyar IPOB ta hanyar kai hare-hare ofishin ƴan sanda tare da kashe jami’an.