Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sake yi w shugaban Najeriya Buhari alurar rigakafin cutar Korona a karo na biyu.

Muhammadu Buhari ya karɓi allurar rigakafin cutar a karo na biyu kamar yadda fadar shugaban ƙasa ta wallafa tare da wasu hotuna.
Tun a watan Marin aka yi wa shugaban allurar rigakafin ta farko kuma a yau Asabar aka sake yi masa karo na biyu.

A watan Maris aka karɓi allurar rigakafin Korona ta Atra Zeneca ƙarƙashin shirin Covax wanda aka yi domin taimakawa ƙasashen Afrika masu ƙaramin ƙarfi.

Har yanzu ba a kai ga krɓar kasha na biyu na rigakafin ba yayin da ake sake yiwa mutanen da aka yiwa ta farko.
Cutar Korona ta sake ɓulla a wasu ƙasashen duniya a karo na biyu wanda har take hallaka mutane.
Ƙasar Indiya it ace ƙasa ta uku da cutar ke yin ta’asa tare da kashe mutane snadin shiga ƙauyuka da cutar ta yi.