Ƙasar China ta sanar da bai wa ma’aurata damar haifar ƴaƴa guda uku ƙasar.

Ƙasar ta yanke hukuncin hakan ne bayan samun alƙaluman da su ka nuna cewar tsofaffi a ƙasar na iya fin matasa yawa.
Kamfanin dillacin labarai na ƙasar Xinhua ya bayyana cewar an ɗauki matakin haka ne bayan wani taro da aka yi ranar Litinin.

Wasu alƙaluma a ƙasar sun nuna cewar adadin mutanen ƙasar bas a ƙaruwa yadda ya kamata a don haka a ka ƙarfafi ƴan ƙasar da haihuwar ƴaƴa guda uku domin gujewa raguwar al’ummarta.

Kafin bayar da wannan dama, an tsaurara doka a ƙasar na haihuwar yara biyu kacal ga ma’aurata.
Ƙasar China ta kasance a sahun gaba-gaba cikin ƙasashe masu arziƙin yawan al’umma a faɗin duniya.