Hukumar kula da shige da ficen kayayyaki a Najeriya Kwastan ta buƙaci mutanen da su ka mallaki jiragen sama a ƙasar da su je domin sabunta rijistar su.

Hukumar ta bayar da wa’adin wata guda domin tabbatar da cewar duk wani mutum da ya mallaki jirgin sama ya je domin tantancewa tare da sabunta rijista.

Hukumar ta ɗauki matakin haka ne da nufin sake inganta fannin tsaro da kuma samawa gwamnati kuɗaɗen shiga.

Akwai  jirage fiye d 100 a ƙasar waɗanda ke zirga-zirga kuma mafi yawa daga ciki na ƴan ƙasar ne.

Mai Magana da yawun hukumar Joseph Atah ya tabbatar da cewar babban abin da ya ja hankalin hukumar ga yin haka shi ne batun da ya shafi tsaro, al’amarin d ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Matsalar tsaro a Najeriya ta zafafa ne tun sama da shekaru 10 da su ka gabata.

Ana zargin wasu jirage na kaiwa ƴan ta’adda makamai a cikin daji, lamarin da ya sa gwamnatin Zamfara dakatar da giftawar jirage a wasu yankunan jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: