Gwamnatin tarayya ta umarci kafafen yaɗa labarai na ƙasar da su rufe shafukan su da ke kan kafar sadarwa ta tuwita.

Hukumar lura da kafafen yaɗa labarai a ƙasar NBC ita ta bayar da wannan umarni na goge shafukan sadarwa na tuwita ga kafafen yada labaran ƙasar.

Hakan ya biyo bayan haramta amfani da shafin a ƙasar wanda gwamnatin ƙasar ta yi sanadin dama da shafin ke bayarwa wanda gwamnatin ta ce hakan barazana ne ga tsaro a ƙasar.

Haka kuma hukumar ta umarci kafafen yada labarai da su daina amfani da shafin a matsayin hanyar samun labarai.

A cewar hukumar NBC doka ta ba ta damar saka doka a kowanne lokaci tare da tabbatar da cewar kafafen yaɗa labarai sun yi biyayya a gareta.

Gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da shafin tuwita a ƙasar sanadin zargin da take na cewar shafin na taimakawa wajen samar da rarrabuwar kai ga ƴan ƙasar.

Haka kuma ya kan bai wa ƴan ƙungiyar IPOB goyon baya mutanen da ke iƙirarin ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar BIAFRA.

Leave a Reply

%d bloggers like this: