Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana taɓarɓarewar tsaro da ake fama da shi a  arewa maso yammacin ƙasar da abu mafi muni da ya addabi kowa kuma shi ma yana damun sa..

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin da ake tattaunawa da shi a gidan talabiji na Arise TV.

Ya ce gwamnonin Arewacin ƙasar sun sha zuwa su sameshi a tare da sanar da shi halin da ake ciki na mataslaar tsaro.

Sai dai ya ce ba komai za a zubawa gwamnatin tarayya ta yi ba akwai matsalolin da gwamnonin jihohi za su iya magancewa.

Haka kuma shugaba Buhari y ace nan ba da jimawa ba zai yi bayani a kan halin da ake ciki a kan tsaro musamman a arewa maso yammacin ƙasar.

A cewar shugaban, akwai tarin nasarorin da ak samu wand azai yi bayani a kan sa.

Ya ƙara da cewa an shirya yan sanda da jami’an soji domin shawo kan matsalar tare da saka al’ummar yabkuna a ciki domin su jagoranci jami;’an tsaro wajen gudanar da aikin tabbatar da tsaro.

Sannan ya ce gwamnatin sa za ta tafiyar da ƴan bindiga da yaren da za su gane.

Ana ci gaba da fuskantar harin ƴan bindiga a jihohi daban-daban na Arewa wanda har ta kai an raba dubban mutane daga matsugunansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: