Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Wajibi Ne Kafofin Sadarwa Su Nemi Lasisi Daga Gwamnati – Lai Mohammed

Ministan yaɗa labarai a Najeriya Lai Mohammed ya bayyana cewar wajibi ne kafofin sadarwa kamar Tuwita da facebook da Instagram su yi rijista da hukuma a ƙasar.

Minsitan ya bayyana haka ne bayan zaman majalisar zartarwa da aka yi jiya a Abuja.

Ya ce tuni aka shiga tattaunawa da kamfanin Tuwita domin ɗage takunkumin da gwamnatin ƙasar ta saka musu.

Daga cikin dokokin da gwamnatin ƙasar ta shimfiɗa akwai tabbatar da cewar kamfanin Tuwita da sauran kafofin sadarwar zamani wajibi ne su yi rijista da hukumar kula da kafafen yaɗa labarai a Najeriya NBC.

Sannan haka kuma ministan ya sake tabbatr da cewar an dakatar da shafin Tuwita a ƙasar ne saboda gudunmawar da shafin ke bayarwa wajen kawo rarrabuwar kai ga ƴan ƙasar.

Sai dai ba a bayyana wa’adin da aka bayar na ganin sauran kafafen sadarwar sada zumunta sun yi rijista da hukumar ba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: