
Saboda maganin taɓarɓarewar harkar siyasa da wasu ‘yan takarar su ke son kawowa a harkokin siyasar Jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi wani gargaɗi mai zafi ga wadanda ke jawo hakan.
Ya yi wannan gargaɗi ne a wani taro da na Sanata Barau I. Jibrin da a ka gudanar a ɗakin taro na Coronation na fadar gwamnatin Jihar, ranar Alhamis, ya ce “Ba za mu yarda da wannan ba. Nine maganin dan takara!

Hakan ta faru ne lokacin da ‘yan banga su ka dinga fito da sanduna a yayin taron Coronation ɗin. Awanni kaɗan kafin wannan kuma a wajen wani taron ƙaddamar aikin titin Gwarzo zuwa Dayi, wanda ya shafi Sanatan na Kano Ta Arewa Barau Jibrin, waɗannan ‘yan banga sun yi ta yin abinda su ka ya dama.

“Mu na gaya muku za a yi babban taro na Dimukuradiyya ranar Asabar. Kuma za mu yi manya manyan baki irinsu Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma Gwamnan jihar Yobe da sauran shugabanni za su halarci wannan babban taro… Saboda haka jam’iyya ta bayar da sanarwa cewar babu tallan dan takara a wannan taro. Ki rike kunnuwanku da kyau. Babu tallan dan takara a wannan taro! in ji Gwamnan.
Ya yi gargadi cewa “Wanda kawai za a yi tallansa a wajen shine Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sai Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, sai kuma Gwamnan Jihar Kano, wanda kun san sunansa.”
A kalmomi masu zafin gaske bisa nuna bacin ransa Gwamnan ya ce, “Babu rike makami a wannan taro! Duk wanda ya rike takobi, ni din nan zan sa a kama shi! Duk wanda ya rike gariyo Gwamna zai sa a kama shi! Duk wanda ya rike adda, Gwamna zai sa a kama shi! Duk wanda ya rike gariyo, Gwamna zai sa a kama shi! Duk wanda ya rike wuka, Gwamna zai sa a kama shi! Duk wanda ya rike sanda, Gwamna zai sa a kama shi!
Ya ci gaba da cewa, “Mun gayawa shugabannin kananan hukumomi cewar motocin da za su zo su tabbata babu kayan fada a ciki. Su tabbata babu manyan hotunan ‘yan takara da za su yi ta dagawa su na kare masu daukar hoto da masu yin bidiyo. Ai ta yawo da wannan, wannan dan takara wannan dan takara wannan dan takara. Kafin ka ankara wancan ya dauko wuka ya sari wannan, wannan ya dau takobi ya sari wancan.”
Cikin nuna rashin jin dadinsa ya sha alwashin cewa, “Wallahi Tallahi ba za mu yarda da wannan ba!!!
Gwamnan ya tunawa jama’a cewa a taron rantsar da shugabannin kananan hukumomi an yi magana har ta kai ba a samu tashin hankali ba. Ya ce “Mu siyasarmu ta Kano siyasa ce mai aiki da ilimi. Siyasa ce mai alkibla. Siyasa ce mai manufa. Ba baki da kunu ba. Ba hanci da majina ba. Ba kafa da kirci ba!
Game da masu nuna nacinsu na yin takarar Gwamna, na ko a mutu ko ai rai ya ce “Mu na tabbatar muku duk ‘yan takarar nan mun fi ku saninsu. Kuma duk dan takara da ya yi hayar ‘yan banga, ya ba su kudi, ya ba su kayan fada, ya ba su makami su ka shigo mana da wata Fasta da dan takara, an sha ganye, an sha wiwi, an sha taba, a ka shiga a na zuga dan takara, ba za mu yarda ba.”
Ya kara tabbatar da cewa “Mu na tabbatar muku Gwamna shine maganin dan takara! Ina fatan kun gane? Duk dan takarar da ya zo ya ba mu kunya a gaban bakinmu, kuma ya jawo a ka sari wani ko a ka yanka wani kuma a ka ba mu kunya gaban bakinmu, ina tabbatar muku ba za mu yarda da wannan ba! Ina fata kunnuwanku a bude suke?!!!
Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Juma’a, 11 Ga Watan Juli, 2021
cps@kanostate.gov.ng
fatimanbaba1@gmail.com