Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce akwai buƙatar gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da talauci a ƙasar ganin yadda mayaƙan Boko Haram ke ɗaukar mutane aiki da kuɗi naira dubu biyar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi yau ranar Demokaraɗiyya a Borno.

Ya ce daga bayanan sirri da suke samu, akwai wasu da suke marawa Boko Haram baya wajen kai musu makamai da wasu kayan buƙatu.

Kuma mayaƙan Boko Haram na biyansu kudi daga naira dubu 5,000 zuwa naira dubu 10,000.

Sannan akwai wasu da su ke kai wa mayaƙan makamai sannan su biya su.

Gwamna Zulum ya ce gwamnatin sa na yin duk mai yuwuwa wajen samar da ayyukan ci gaba, amma har yanzu akwai tsoro da ke cikin zukatan al’ummar jihar saboda fargabar Boko Haram.

Sama da shekaru 10 ake fuskatnar rikicin Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya.

Dubban mutane aka kashe yayin da wasu su ka rabu da muhallin su a sanadin rikkicin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: