Yayin da shugaban Najeriya ke ziyaratar Maiduguri a gabashin ƙasar a Arewa Maso Yamma kuwa an sace ɗalibai mata tare da kashe mai gadi.

An sace ƴan matan ne a wata kwaleji da ke Birnin Yauri a jihar Kebbi.
Rahotannin da su ke samun mu a wannan lokaci sun nuna cewar ana zargin ɗalibai matan da aka sace na da yawa.

Ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata a wata makaranta kwalejin tarayya da ke Yawuri a jihar Kebbi yau Alhamis.
ƴan bindigan sun je makarantar ne a kan babura ɗauke da bindigu sannan su ka fara harbin jami’an tsaron da ke gadin makarantar.

An sace ɗalibai mata da maza su 30 sai malamansu guda uku.
Wani hsiadar gani da ido ya shaida cewar an tafi da wadanda su ka samu raunin harbi zuwa asibiti domin duba lafiyarsu.
Daga cikin waɗanda aka harba har da ɗalibai a ciki.
Wasu daga cikin ɗaliban sun bazu jikin daji domin tsira da rayuwarsu.
Ƴan bindigan sun kwace motar ƴan sandan da ke gadin makarantar sannan su ka tafi da daliban.
Ƴan bindigan sun yi amfani da motar ƴan sandan wajen zuwa wasu daga cikin ɗaliban da su ka sace.