Hukumar lafiya matakin farko a Najeriya ta bayyana cewar nan da watan Agusta na shekarar da muek ciki za ta sake karɓar kasha na biyu na allurar rigakafin cutar Korona.

Babban darakta a hukumar Dakta Faisal SHu’aib ne ya bayyana haka a yayin da ake taron mako-mako don bibiya a kan al’amuran da ke tafiya dangane da rigakafin cutar Korona a ƙasar.
Ya ce akwai yuwuwar a sake kawo rigakafin Astra Zeneca a ƙarshen watan Yuli mai kamawa ko kuma farkon watan Agusta.

Rigakafin da za a kawo za ta kai miliyan 3.92.

Daraktan ya ƙara da cewar akwai mutane miliyan 1,978,808 waɗanda aka yi wa allurar rigakafin a Njeriya yayin da aka yi wa mutane 680,345 kashi na biyu na allurar.
An sake bude shafin rijistar yin allurar rigakafin ga mutanen da su ka kai shekaru 18 zuwa sama.
Dakta Faisal ya yi kira ga ƴan Najeriya da su bayar da haɗin kai domin tabbatar da cewar an yi musu allurar don rage aduwar cutar a Najeriya.