Rundunar ƴan sanda a jihar Kaduna sun yi nasarar kama wani da ake zargi da aikata garkuwa da mutane bayan musayar wutsa a tsakanin su.

Ƴan sandan sun kama mutumin ne a wani daji da ke saminaka a ƙaramar hukumar Lere ta Kaduna.

Kakakin yan sandan jihar ASP Muhammad Jalige ne ya bayyana hakan wanda ya ce mutumin da aka kama na da alaƙa da waɗansu manyan masu garkuwa a Kaduna.

Sannan sun samu bayanai daga gareshi wanda zai taimaka wajen kama sauran ƴan bindigan da ke ɓoye a dazukan jihar.

An kama mutumin mai suna Bello Abubakar a jiya yayin da ƴan sanda ke gudanar da sintiri.

Tuni aka ci gaba da gudanar da bincike a kansa tare da neman wasu bayanan sirri waɗanda za su taimawa jami’an tsaro.

Yayin da aka kama wanda ake zargi an sameshi da bindiga ƙirar AK47 a cikin wata mota ƙirar Golf.

An ɗauki tsawon lokaci ana ayyukan ta’addanci a Kaduna musamman satar mutane, satar shanu da fashi da makami.

Leave a Reply

%d bloggers like this: