Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar kuɓutar da ɗalibai bakwai cikin sama da 30 da aka sace a kwalejin tarayya da ke Yawuri ta jihar Kebbi.

A yayin wani luguden wuta da sojojin su ka yi wa ƴan bindigan, sun kashe wasu daga cikin su.
Haka kuma rundunar tya kwato dabbobi 800 wanda ƴan bindiga su ka sace.

Amma wasu daga cikin ɗaliban da aka sace sun mutu a yayin da ake yin musayar wuta tsakanin sojoji da yan bindiga.

ɗalibai uku ne su ka mutu a cewar wani mazaunin garin wanda y ace mata biyu ne mace guda.
Amma rundunar sojin ta ce ɗaliba ɗaya ta mutu a yayin da suke ƙoƙarin ceto su.
Ƴan bindiga sun shiga makarantar kwalejin tarayya da ke yawuri a ranar Alhamis da hantsi sannan su ka tafi da wasu daga cikin su.
A yayin da ƴan bindigan su ka je makarantar sun kwace motar jami’an tsaro sannan su ka yi amfani da ita wajen zuba ɗaliban tare da tafoya da su cikin daji.
Haka kuma akwai ɗalibai da dama da su ka samu raunin harbi yayin da yan bindigan su ka je.