Helkwatar rundunar tsaro a Najeriya ta ce jami’an sojin ƙasar sun kashe mayaƙan Boko Haram sama da ashirin a jihar Borno.

Mai Magana da yawun helkwatar tsaro a Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar.

Ya ce rundunar sojin ƙasar ce ƙarƙashin dakarun Opretion Haɗin Kai su ka kashe mayaƙan a sansaninsu.

An kai wa mayaƙan Boko Haram ɗin farkaki a a sansaninsu da ke dajin a jiya Lahadi.

Harin da sojojin su ka kai ya boyo bayan wani bayanan sirri da su ka samu a kan mayaƙan Boko Haram ɗin.

Yayin da su ka kai harin, sun kwato wasu bindigu da mota mai bindiga guda biyu da bindigu ƙirar AK47 guda uku sai wasu motoci da su ka lalata.

A cewar kakakin, dakarun sojin sama ne su ka yi wa mayaƙan luguden wuta lamarin da yay i sanadiyyar kashe ƴan Boko Haram sama da 20 tare da kotrar wasu daga cikin dajin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: