Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya yi zargin mutanen da ke satar mutane an ɗauke su haya ne domin haifar da fitina a Najeiya.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya kafa gungun jami’an tsaro dubu ɗaya wadanda aka ware su don ceto ɗaliban makaranatar Islamiyya da aka sace.

Gwamnan ya ce mutanen da ke satar mutanen a Najeriya ba ƴan ƙasar bane ana amfani da su ne wajen haifar da fitina ne a ƙaar.

Abubakar Sani Bello ya ce wajibi ne a tashi tsaye wajen yaƙi da su da ma wadanda ke basu bayanai domin abin da ke faruwa shiryayyen al’amari ne.

A baya gwamnan ya ziyarci wasu daga cikin iyayen ɗaliban da aka sace har ma ya musu alƙawarin ceto ƴaƴan nasu cikin ƙoshin lafiya.

An shirya gungun jami’an tsaro guda dubu ɗaya waɗanda su ka haɗa da sojoji ƴan sanda da jami’an hukumar kare fararen hula sai jami’an sa kai na bijilanti.

Ƴan bindiga sun sace ɗaliban makarantar islamiyya ta Salihu Tanko da ke Tegina a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Daga cikin ɗaliban da aka sace akwai yara ƴan ƙasa da shekaru biyar a duniya.

Ɗaliban da aka sace su sama da 130 ne sai dai yan bindigan sun buƙaci basu kudin fansa naira miliyan 150 kafin sako ɗaliban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: