Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta shirya tsaf don ci gaba da yin rijistar katin zaɓe na din-din-din ga ƴan ƙasar.
A cikin shirye-shiryen hukumar, ta samar da ma’aikata 5,346 waɗanda za su yi aikin rijistar a euraren yin rijistar 2,346 na Najeriya.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka yayin gabatar da tsarin yin rijistar zaɓen a yanar gizo.
Sannan an samar da kayan aikin yin rijistar zaɓen domin ci gaba da yi wa ƴan ƙasar.
Farfesa Yakubu ya ƙara da cewa ƙara adadin yawan wuraren yin rijistar ne la’akari da yawan al’ummar ƙasar a yanzu.
Daga cikin kayan aikin akwai wadanda aka zamanantar ta hanyar amfani da kimiyyar zamani tare da sauƙaƙa aikin.
Kuma za a ci gaba da yin rijistar katin zaɓen ne daga ranar 28 ga watan da muke ciki.