Hukumar kare farare hula  aNajeriya ta aike da dakarunta mata domin kula da makarantu daga masu satar mutan.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta samu umarnin haka ne daga ma’aikatar harkokin cikin gida wanda ta umarci fito da tsarin don tsare makarantu da ɗalban.

Shugaban Hukumar ta ƙasa Ahmed Audi ne ya bayar da umarnin tattara jami’an a johohi daban-daban tare da basu horo na wata guda ka yadda za su tsare makarantun.

An tura jami’an tare da basu kayan aiki domin kawo ƙarshen satar ɗalibai a Najeriya.

A baya sai da hukumar ta bayyana adadin makarantu mafi yawa da ka iya fuskantar hari daga ƴan bindiga.

A Arewacin Najeriya ana fama da kai hare-hare makarantu waɗanda ake sace ɗalibai da malamai a wasu lokutan ma a kai ha halaka wasu tare da jikkatawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: