Hukumar kiyaye afkuwar haɗdura ta ƙasa a Najeriya FRSC ta nesanta kanta daga wani shafin yanar gizo da ake turawa da nufin ɗaukar ma’aikata ko sakin sunayen ma’aikatan da aka ɗauka.

Kakakin hukumar a Najeriya Bisi Kazeem ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar yau alhamis a Abuja.
Hukumar ta ce sam wannan shafi da aka ƙirƙira ana amfani da shi ne don yin damfara ba daga wajen su yake ba.

Haka kuma hukumar ta ja hankalin al’umma da su kasance masu taka tsan-tsan ga irin shafukan yanar gizon da ake turawa da sunan hukumar.

Sannan ta nanata cewar akwai hanyoyin kafafen yaɗa labarai amintattu da suke amfani da su idan shirin hakan ya taso.
Wasu shafuka ne a kafar Intanet da ake turawa da sunan ɗaukar ma’aikata a hukumar ko kuma duba sunayen mutanen da aka ɗauka aiki a hukumar wanda ta ce sam ba ta san da shi ba.