Hukumar Zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano ta kammala aikin ƙara mazaɓu don sauƙaƙwa jama’a wajen kaɗa ƙuri’a.
Kwamishinan zaɓe a jihar Kano Riskuwa Arabu Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ce a halin yanzu akwai mazaɓu guda 3,148 yayin da aka samu ƙarin akwatin zaɓe guda 11,222.
Wannan wani mataki ne na auƙaƙawa masu zaɓe don rage cunkoso tare da bai wa kowanne ɓangare dama wajen cin moriyar demokaraɗiyya.
Haka kuma akwai rumfunan zaɓen da aka sauyawa wuri guda 38, daga ciki akwai wuraren ibada, da masarautu da sauransu.
Hukumar ta ce ta shirya tsaf don fara aikin rijistar katin zaɓe, daga ranar 28 ga watan da muke ciki, sannan aka sanya ranar 19 ga watan Yuli a matsayin ranar da za a fara bayar da rana don ziyartar wuraren da ake rijistar domin ƙarasa ɗaukar bayanan da aka tsara za a karɓa.
Haka kuma akwai dama na aika bayanai ta hanyar intanet, sannan za a sanar da ranar da za a fara bayar da katin zaɓen a nan gaba.