Ƙungiyar masu gidajen biredi a Najeriya sun yi barazanar ƙra farashin biredi a ƙasar bisa hauhawar farashin fulawa.

Ƙungiyar ta ce ba ta da wani zaɓi illa ƙara farashin b iredin sanadin farashin fulawa da yay i tashin goron zabi.
Sakataren ƙungiyar Kabiru Hassan Abdulahi ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai jiya Juma’a Kano.

Ya ce ƙungiuyar ta yi ƙoƙarin zama da kamfanonin da su ke samar da fukawa a ƙasar don ganin an sassuta farashin ta.

Ya ce shekarar 2020 da ta gabata ana siyar da buhun fulawa a kan kudi naira dubu tara yayin da yanzu farashin ya kai naira 16,000.
Ƙungiyar za ta tattauna da sauran mambobinta domin cimma matsaya a kan ƙara farashin biredin a cikin kwanaki goma.
Haka na zuwa ne kwanaki kaɗan da masu siyar da gurasa a Kano su ka yi barazanar tsunduma yyajin aikin saboda ƙarin farashin fulawa.