Hukumar samar da shaidar katin ɗan ƙasa a Najeriya ta sanar da cewar ta kammalawa mutane miliyan 57.3 rijistar katin su a fadin ƙasar.

Babban darakta a hukumar Aliyu Aziz ne ya bayyana haka yayin da aka gudanar da taron ƙarawa juna ilimi yau a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce a cikin mutane sama da miliyan 200 a Najeriya ƙasa da mutane miliyan 60 ne kadai su ka mallaki katin ɗan ƙasa.

Taron ya mayar da hankali ne a kan hanyar da za a bi don inganta rijistar a yanar gizo wanda aka shirya a Abuja.

Hukumar sadarwa a Najeriya ta bayar da umarnin hada lambar dan ƙasa da layukan kira na wayar salula a wani salon a taimakawa tsaro a ƙasar.

Sai dai ta sha tsawaita wa’adin da ta saka don rufe layukan da ba a yi musu rijista ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: