Wasu mafarauta haɗin gwiwa da jami’an sa kai na Bijilanti sun kama wani da ake zargi mai garkuwa da mutane ne.

Mafarautan sun kama mutumin ne a ranar Juma da yammaci,

Jami’an sa kai sun kama mutumin bayan musayar wuta da su ka yi a tsakanin su.

Ƴan bindigan na shirin kai hari a kan matafiya da ke bin hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Bayan musayar wuta da su ka yi tsakanin mafarautan da ƴan bindigan, sun kama ɗaya daga cikin gungun ƴan bindigan.

Sannan sun samu damar kwato wata bindiga ƙirar AK47 daga hannun wadanda aka kama.

Ko a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, sai da mafarautan su ka kama masu garkuwa da mutane a dajin da ke tsakanin babbar hanyar Lokoja zuwa buja.

Babban mai taimakawa gwamnan Kogi a kan ayyuka na musamman ya tabbatar da faruwarv lamarin tare da miƙa wadanda ake zargi zuwa ga ɓangaren ƴan sanda don gudanar da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: