Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da kama jagoran ƙungiyar IPOB Nnamdi Kanu.

Ƙungiyar IPOB masu fafutukar ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar BIAFRA.

Ministan Shari’a a Najeriya Abubakar Malami SAN ne ya tabbatar da hakan yau a Abuja bayan wani taron manema labarai.

Ya ce an kama Nnamdi Kanu ne tun ranar Lahadi sannan za su gurfanar da shi a gaban kotu a kan zargin da ake masa.

Nnamdu Kanu ne bisa zargin cin amanar ƙasa tare da kafa wasu ƙungiyoyin da ke tayar da fitina ciki har da jagorantar ƙungiyar IPOB ƙungiyar da jami’an tsaro su ka ayyana a matsayin yan ta’adda.

Bayan kama shi a farko, a shekarar 2017 aka bayar da belin sa amma ya tsallake sharuɗan belin wanda kotu ta soke belin a shekarar 2019.

Nnamdi Kanu na amfani da kafafen sadarwar zamani wajen tunzura magoya bayansa don ganin sun ci gaba da tayar da fitina musamman a kudu maso gabashin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: