Bisa hauhawar farashin ɗanyan mai a kasuwar duniya, a na iya siyar da mai a kan naira 256 duk lita guda a halin yanzu, sai dai babu wannan shirin ƙarin a watan da za mu shiga.
Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya sanar da cewar bas hi da shirin ƙara farashin mai a watan Yuli mai kamawa.
Shugaban kamfanin a Najeriya Mele Kyari ne ya bayyana haka a yayin tattaunawar sa da gidan talabiji na Channels.
Ya ce har yanzu farashin mai yana nan a kan naira 162 yayin da mutane ke siya a kan naira 165.
Ya ƙara da cewar, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya bayar da umarnin haka na ganin cewar antabbata an bi dukkan hanyar da doka ta tanada na ganin ba a ƙara farashin man fetur ɗin a wannan lokaci ba.
Sannan akwai matatun mai da za a ci gaba da aikin su a ƙasar wadanda za su taimaka don sauƙaƙa tsadar man.
Tun a baya akwai ƴan Najeriya ke tunanin za a ƙara farashin man fetur din har ta kai wasu sun fara sukar batun duba ga halin matsin da jama’a ke ciki.