Wata babbar kotu a jihar Kaduna ta sanya ranar 28 ga watan Yuni da muk ciki a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a kan shari’ar da ake yi wa shugaban mabiya Shi’a Ibrahjim Zakzaky da mai ɗakin sa Malama Zinat.

Gwamnatin jihar Kaduna ce ta gurfanar da Malamin a gaban kotu bayan tare da tuhumarsa da zargin kisan kai da kuma hada taro ba tare da izini ba.
Tsawon shekaru aka kwashe shugaban mazahabar shi’a Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa Malama Zinat ke hannun hukumar tsaro da DSS duk da cewar kotu ta bayar da belin sa.

Sai dai lauyoyin Ibrahim Zakzaky sun buƙaci kotu ta yi watsi da ƙarar saboda gaza gabatar da hujja a kai.

Amma lauyoyin gwamnati sun buƙaci a ci gaba da shari’ar saboda hujjar da su ka gabatar wa da kotu.
Tun bayan kama shugaban mabiya shi’a a jihohi daban-daban ke gudanar da zanga-zanga don ganin an saki malamin nasu.
Mabiya shi’a sun yi zargin gwamnati da ƙin barin shugaban domin samun kyakkyawar kulawa daga likitocin da za su duba lafiyar sa.
Barista Huruna magashi wani lauya daga ɓangaren Ibrahim Zakzaky ya bayyana cewar daga cikin shaidun da ɓangaren masu ƙara su ka gabatarwa kotu har guda 15 babu wadda aka samu da alaƙa da zargin da ake yi wa shugaban Shi’a Ibrahim Zakzaky da mai ɗakin sa Malam Zinat.
A kan hakan ne lauyoyin ɓangaren Ibrahim Zakzaky ƙarƙashin jagorancin Barista Femi Falana su ka miƙa roƙo ga kotun don ganin ta rufe shari’ar tare da watsi da zragin da ake masa.